IQNA

Tarihin Manzon Allah Ita Ce Babbar Hanyar Riko Ga Al'ummar Islama

Bangaren siyasa da zamantakewa; malummai a afganistan sun yi nuni da Sirar Manzon Allah (SWA) a matsayin sakon sulhu da imani da jaddada cewa: riko da Sirar Manzo (SWA) it ace babbar hanyar al'ummar islama.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna a Afganistan ce ta watsa labarin cewa; malumman masallatan juma'a a wannan kasa ne suka shirya wannan taro da lokacin suka yi bayani dalla-dalla kan hanyoyin da za su taimakawa dan adam ya magance irin matsalolin da suke addabarsa da cewa babu wata hanya mafi dacewa da ta fit a bin sirar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.Kuma dubban musulmi ne suka halarci gurin gudanar da wannan taro saboda muhimmancin abubuwan da aka tattauna a kansu a gurin taron.

378265