IQNA

An Gudanar Da Wani Zama Kan Ilimomin Falsafa Da Irfani A Bolgaria

Bangaren Fikira da ilimi: An gudanar da wani zama na musamman a kasar Bolgaria domin yin bahasi kan ilmomin Falsafa da Irfani, wanda reshen cibiyar kula da nazarin addinin Musulunci ta kasar Iran da ke Bolgari a ya shirya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an gudanar da wani zama na musamman a kasar Bolgaria domin yin bahasi kan ilmomin Falsafa da Irfani, wanda reshen cibiyar kula da nazarin addinin Musulunci ta kasar Iran da ke Bolgari a ya shirya. Babban masanin falsafan nan na kasar Bolgari a(Toddor wa) shi ne babban bako wanda ya bude taron da jawabinsa, inda ya nuna muhimmancin da ke tattare da Irfani a duniya tare da hada shi da falsafa, ya ce a lokacin da mutum ya fahimci manoni da ke cikin ilmomin biyu, to ko shakka babu zai samu ruhinsa da samuwarsa a cikin wata duniyar ta daban. Ya kara da cewa ilmomin biyu danfare suke da juna kuma ba za a raba su ba, domin kuwa kowannensu yana agazawa dayan ne.


379552