IQNA

Gasar Karatun Kur'ani Ta Canja Mahangar Wasu Kasashe Dangane Da Iran

13:14 - March 19, 2009
Lambar Labari: 1757613
Bangaren kur'ani: Wani makarancin kur'ani na kasa da kasa daga kasar Tanzania ya bayyana cewa; gudanar da gasar karatun kur'ani ya canja mahangar mutane da kasashe da dama na mabiya mazhabobin sunna dangane da Iran da ma mazhabar shi'a.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya zanta da wani makarancin kur'ani na kasa da kasa daga kasar Tanzania, da ya halarci gasar da jami'ar Mostafa ta shirya kan karatun kur'ani da hadisan manzon Allah (SAW) inda ya bayyana cewa; gudanar da gasar karatun kur'ani ya canja mahangar mutane da kasashe da dama na mabiya mazhabobin sunna dangane da Iran da ma mazhabar shi'a, domin kuwa a cewarsa wasu daga cikin musulmi mabiya mazhabobin sunna suna da karancin masaniya kan mazhabar shi'a, lamarin bai ma tsaya a nan ba, a'a an yi ta yi musu farfaganda dangane da mazhabar shi'a da Iran, lamarin da ya sanya su kyamar duk wani abu da ya danganci shi'a ko Iran, bisa zaton cewa shi'a na da kur'aninsu na daban, ko kuma suna kiyayya da manzon Allah, amma lokacin da mutum ya zo Iran zai ga masoya kur'ani kuma masoya manzon Allah na gaskiya.

377884


captcha