Bangaren siyasa: hdarat ayatullahi Khamnai a cikin sakon taya murnar shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiya da fatar al'ummar kasar za su jurewa duk wani canji da sauyi da ke tattare da wannan sabuwar shekara ya kara da cewa:bisa la'akari da muhimmanci rayuwa da tushen saye da sayarwa cikin hankali da kare amfanin kasa wannan sabuwar shekara ya sanya mata sunan shekarar gyara kura-kura na almubazzaranci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a iran Ikna ce ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta ofishin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran ta watsa rahoton cewa; jagoran bisa la'akari da muhimmancin kusancin wannan sabuwar shekara da ranar maulidi ta tunawa da ranar haifuwar fiyayyen halitta manzon Allah manzon rahama Muhammadu dan Abdullah (SWA) da kuma ranar haihuwar jikansa Imam Ja'afar Sadik (AS) ya taya al'ummar Iran murnar wadannan raneku masu muhimmanci da fatar Allah ya albarkaci wannan sabuwar shekara da alheri da sa'ada.Jagoran juyin juya halin musuluncin ya yi nuni da abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata ta 1387 a cikin Iran da wajen kasar da faraway da ci gaban da Iran ta samu ta fuskar makamashi da ci gaban ilimi da jefa tauraron dan adam a cikin sararin samaniya mai suna Umid dam asana Iraniyawa suka kera karkashin dogaro da kai.Har ila yau ya yi nuni da cibiyar makamashi ta Bushahar da ta fara aiki na gwaji makamshi don ci gaban kasar da al'ummarta a dukan bangarori ko shakka babu da hakan ba zai yi wa makiya dadi bad a bakanta masu da rai.Jagoran ya yi nuni da majalisar shawara ta takwas da yadda suka aiwatar da ayyukan alheri tare da gwamnatin zartarwa tare da fatar aiki tare tsakanin majalisa da gwamnati ya ci gaba da wanzuwa. Dangane da ketare kuwa ya yi nuni da abubuwan da suka faru a yankin Gaza da HKI ta nuna rashin tausayi kan kananan yara da mata da cewa kowa ya ga yadda HKI ta kasha kananan yara da mata da tsaffi a harin kwanaki 22 da ta kai wa wannan yanki na Gaza.Amma dangane da wannan shekara sabuwa ta 1388 da ya bata sunan gyara kan almubazzaranci ya yi fatar al'ummar Iran za su daidaita rayuwarsu da yi mata tsari da kawo sauki wajen saye da sayarwa da tausayin na kasa da kuma rage yawan amfani da wutar lantarki ba kan ka'ida bad a rowan sha da dai sauransu.
379946