Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Associated press cewa; gwmantin Morocco ta dauki tsaurarn matakai wajen takura mabiya mazhabar shi'a a kasar, bisa hujjar dakushe kaifin tasirin addini a tsakanin jama'a. Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar Morocco sun bayyana cewa; jami'an tsaron kasar bisa umurnin gwamnati suna ci gaba da kame mutane garuruwan da ke arewacin kasar, sakamakon karbar mazhabar shi'a da suka yi.
A ranar Asabar da ta gabata ma gwamnatin Morocco ta rufe wata makarantawar Irakawa da ke birnin Ribat bisa hujjar cewa ana koyar da hukunce-hukuncen mazhabar shi'a a cikin makarantar. A 'yan makonnin da suka gabata ne gwamnatin Morocco ta yanke dangantaka tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bisa hujjar cewa Iran na da hannu wajen yaduwar mazhabar shi'a a cikin kasar.
380224