A wata zantawa da hada kamfanin dillancin labaran Ikna ya gudanar tare da wani makarancin kur'ani na kasa da kasa daga jamhuriyar Musulunci ta Iran (Mehdi Adli) ya bayyana cewa; yin amfani da salon karatun kur'ani na Mustafa Isama'il na da tasiri na musamman a cikin zukatan masu karatu da kuma masu saurare. Ya ci gaba da cewa; Mustafa Isma'il mutum ne da ya shahara ta fuskacin karatun kur'ani ta hanyar kyautata sauti da kiyaye ka'idojin karatun kur'ani, kuma wasu suna sauraron karatunsa ne saboda hakan, amma bayan haka akwai abubuwa da suke tattare da shi na baiwa wanda mutane da dama ba su gano ba sai bayan rasuwarsa, daga ciki kuwa har da tasirin da kira'arsa ke bari a cikin mai kwaikwayon karatunsa da kuma mai sauraron karatun, domin kuwa karatun yana jan hankali zuwa ga ma'anar ayoyin da yake karantawa, domin kuwa shi kansa yana karanta ayoyin bisa la'akari da ma'anoninsu.
374620