IQNA

Kayatarwar Da Ke Cikin Sinima Da Ke Tattare Da Manufofi Na Addini

Bangaren fasaha: Sinima da ake shiryawa kan manufa ta addini da ta ginu kan koyarwa ta kur'ani, ta banbanta da sauran shirye-shiryen sinima da ake shiryawa ba a kan manufa ta daddini ba ta fuskoki da dama.
A wata zantawa da kamfanin dillancin labaran Ikna ya gudanar tare da wani dan wasan sinima na kasar Iran (Mehran Rajabi) ya bayyana cewa; sinima da ake shiryawa kan manufa ta addini da ta ginu kan koyarwa ta kur'ani, ta banbanta da sauran shirye-shiryen sinima da ake shiryawa ba a kan manufa ta daddini ba ta fuskoki da dama.Ya ci gaba da cewa sinima da ake shirya a jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha banban da sinima da sauran sinima da ake shiryawa a wasu kasshe, domin kuwa dukkanin shirye-shiryen sun ginu ne a kan manufa ta addini da koyarwa ta alkur'ani mai tsarki, ta yadda ake kiyaye dabi'u kyawawa wadanda Musulunci yake koyar da bil adama, kuma a lokaci guda ta wannan hanyar sinimar tana isar da sakonta a cikin rayuwar zamantakewar jama'a, siyasa, tattalin arziki da dai sauransu.

380214