Bangaren kasa da kasa: Ya zuwa yanzu sama da palastinawa marassa lafiya dari uku ne suka riga mu gidan gaskiya a zirin Gaza, sakamakon ci gaba da killace yankin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila da gwamnatin Masar ke yi wa yankin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Ma'an) cewa; ministan kula harkokin kiwon lafiya a halastacciyar gwamnatin Hamas Yusuf Mudlil ya sanar cewa; ya zuwa yanzu sama da palastinawa marassa lafiya dari uku ne suka riga mu gidan gaskiya a zirin Gaza, sakamakon ci gaba da killace yankin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila da gwamnatin Masar ke yi wa yankin. Ya ci gaba da cewa ya zama wajibi a kan sauran kasashen duniya da su taka rawa wajen kawo karshen killacewar da al'ummar Gaza ke fama da ita, ya ce a cikin 'yan makonnin nan sama da fararen hula marassa lafiya ashirin ne suka rasa rayukansu a Gaza, sakamakon kilacewar da suke fama da ita, aka sarinsu kuma kanan yara ne, ya kara da cewa yanzu haka sama da marassa lafiya dubu daya ne suke jiran a basu damar fita daga Gaza zuwa wasu kasashe domin samun magani, domin kuwa asibitocin Gaza ba za su iya yi musu magani ba, amma har yanzu babu izini daga Haramtacciyar Kasar Isra'ila da gwamnatin Masar Ba su bayar da izinin fita da mutanen zuwa wajen Gaza domin samun magani ba, wace wannan kadan ne daga cikin irin mawuyacin halin da al'ummar Gaza suka samu kansu a cikinsa ne sakamakon killacewar da aka yi musu.
380238