IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Matsayin Imam Ali (AS) Birnin Tirana

Bangaren al'adu da zamntakewa: An gudanar da wani taro na yini guda a birnin Tirana fadar mulkin kasar Albania dangane da rayuwar Imam Ali (AS) da kuma yadda za a yi koyi da shi a cikin dukkanin bangarorin na rayuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an gudanar da wani taro na yini guda a birnin Tirana fadar mulkin kasar Albania dangane da rayuwar Imam Ali (AS) da kuma yadda za a yi koyi da shi a cikin dukkanin bangarorin na rayuwa. Rahoton ya ci gaba da cewa babban kwamitin kula da aharokin musulmin yankin Balkan shi ne ya shirya gudanar da taron a birnin Tirana na kasar Abania, inda taron ya samu halartar masana daga mabiya addinin Musulunci da kuma mabiya addinin kiristanci daga kasashen turai daban-daban na turai da Asia, da suka hada da kasashen Faransa, Albania, Makdunia, Bolgaria, Kossovo, Rasa, Turkia Iran da dai sauransu. Shugaban kwamitin (Haji Salim Moga) ya bayyana cewa; wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan taron, kuma ya bayyana fatar ci gaba da gudanar da shi a wasu lokuta masu zuwa a nan gaba, ta yadda hakan zai zama wata hanya ta samun fahimtar juna tsakanin al'ummomi daban-daban na duniya.

380246