Bangaren Siyasa da zamantakewa: A karon farko an kafa wani asibitin tafi da gidanka karkashin hubbaren Sayyid Yahya(AS) jikan manzon Allah (SAW) a kasar Afganistan, wanda ya ya hada dukkanin bangarori na likitanci da ake bukata domin bayar da agajin gaggawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a karon farko an kafa wani asibitin tafi da gidanka karkashin hubbaren Sayyid Yahya(AS) jikan manzon Allah (SAW) a kasar Afganistan, wanda ya ya hada dukkanin bangarori na likitanci da ake bukata domin bayar da agajin gaggawa. Shugaban kungiyar bayar da agaji ta Helal Ahmar ta kasar Iran reshen kasar Afganistan ya bayyana cewa; kungiyar bayar da agajin ta Helal Ahmar ta kasar Iran ta taka rawar gani wajen samar da wannan asibi, kuma yanzu haka ana kokarin kara fadadata domin amfanar al'ummar lardin Sabol da kewaye, ya ce ya tattauna da al'ummar lardin wadanda suka bayyana masa matukar farin cikinsu dangane da wannan aiki mai matukar muhimmanci da aka gudanar, kuma sun yi alkawalin bayar da dukkanin gudunwamawa wajen ganin ayyukan asibitin sun ci gaba, da kuma ci gaba da bayar da gudunmawa wajen kara gyara hubbaren Yahya (AS) jikan manzon Allah (SAW) da ke yankin.
379848