IQNA

Iran Kasa Ce Mai Tasiri Wajen Yaki Da Sahyuniyanci

12:28 - March 26, 2009
Lambar Labari: 1758059
Bangaren Siyasa da zamantakewa: Mataimakin sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah a kasar Labanan (Sheikh Na'im Kasim) ya bayyana cewa; Iran ta taka rawa mai abban tasiri wajen yaki da sahyuniyanci, da kuma hada kan musulmi da kiritoci a kasar Labanan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-mustakabal) ta kasar Labanan cewa; a cikin wanin bayani da mataimakin sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah Sheikh Na'im Kasim ya gabatar ya bayyana cewa; Iran ta taka rawa mai abban tasiri wajen yaki da sahyuniyanci, da kuma hada kan musulmi da kiritoci a kasar Labanan, Na'im Kasim ya bayyana hakan ne a wani taro da aka shirya domin yin nazari kan tunanin wasu manyan mutane da suka bayar da gudunmawa ga gwagwarmayar Labanan wajen kalubalantar yahudawan sahyuniya da akidarsu ta zalunci da mamaye, da suka hada da (Sheikh Abdullah Al'alali) da kuma (Imad Mogniyah) wadanda suka taka rawa wajen wayar da kan al'ummar Labanan da ma yankin baki daya wajen shiga kafar wando daya da munanan manufofin gwamnatin Haramtcciyar Kasar Isra'ila, wanda hakan ne ya kai su ga yin shahada a hannun yahudawan shayuniya. Ya ce musulmi za su iya yin amfani da tunanin wadannan manyan malamai kuma masana guda biyu wajen samun hadin kai tsakaninsu.

380204
captcha