IQNA

Nabiyi Birri: Kur'ani Na Jaddada Hadin Kai Tsakanin Addinai

Bangaren siyasa da zamantakewa: Nabiyi Birri shugaban majalisar dokokin kasar Labanon ya yi nuni da karfin musulmi wajen samarwa da kare hadin kai da karfafa hakan musamman Kur'ani da ke jaddada hadin kai a tsakanin addinai.
Daga labanon ne cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar almustakbal a wannan kasa ta watsa rahoton cewa: Nabiyi Birri ya yi wannan bayani ne a wani taron kasa da kasa na masana da binciken abubuwan da Shekh Abdullah Alayali da sheikh Muhammad Jawad mugniya manyan masana malummai a duniyar musulmi da suka karfafa hadin kai da wanzar da shi a tsakanin musulmida cewa addinin musulunci na kara karfi ne wajen samara da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin addinai.Shugaban majalisar dokokin kasar ta Labanon ya bayyana cewa: albarkacin tunanin wadannan masana neaka samara da Hauzar neman sani da fahimta a birnin Beirut da ta yada addini da hadin kai.Ya kara da cewa : Ana bukatar hadin kai da tunawa da manyan masana da malummai da suka gabata da suka yi aiki a wannan fage kamar Imam Musa Sadre jagoran yan Shi'a a kasar Labanon day a karfafa wannan manufa ta hadin kai.

380203