IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Binciken Hanyoyin Jaddada Hadin Kai A Tsakanin Musulmi

Bangaren siyasa da zamantakewa: A jiya ne aka bude taron binciken abubuwa masu kima da manyan malumai Sheikh Abdullah Alayile da Sheikh Muhammad Jawad Muniya da suka sadaukar da rayuwarsu da lokutansu wajen samara da hadin kan musulmi.
Daga Labanon ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Almustakbal a wannan kasa ta watsa labarin cewa; a wannan taro na kwanaki biyu da ofishin da ke kula da yada al'adun Jamhuriyar musulunci tai ran ta shirya a kasar ta Labanon tare da hadin gwiwar cibiyar kara kusanci tsakanin mazhabobin musulunci da hadin guiwarcibiyoyin Imam Sadik (AS)mahalarta taron za su yi bincike kan abubuwa masu kima da wadannan masana biyu musulmi suka bari domin bin hanyoyin karfafa hadin kai a tsakanin musulmi.A wajen wannan taro an samu halartar manyan baki kamar Sheikh Na'im Kasim mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah a Labanon,nabiyi Birri shugabana majalisar dokokin kasar Labanon,Muhammad Rida Shibani jakadan Jamhuriyar musulunci a Labanon,Muhammad Huseini Ra'is Zade mai kula da ofishin yada al'adun Iran a labanon da kuma Sheikh Muhamma yazbak wakilin Jagoran juyin juya halin musulunci da kuma Fauzi Salukh ministan harkokin wajen labanon da wasu manyan yan siyasa da malumman addini da na jami'o'I a wannan kasa.

380202