Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa; Alkur'ani a tsawon tarihi ya karawa al'ummar musulmi karfin gwiwa a bangare guda ya karyawa makiyan addinin musulunci da musulmi gwiwa da mayar masu da aniyarsu a kokarinsu na ganin bayan wannan addini a tsawon tarihi.Al'ummar musulmi ta hanyar koyarwa ta Alkur'ani ta samu rayuwa mai inganci da karfi a ciki da wajenta.Saboda haka matasa a yau da masu zuwa a nan gaba sunada jan aiki da ke jiransu day a kamata su kara wannan matsaya da kuma yin riko da haka domin ci gaba da fuskantar makiyansu dab a su barci dare da rana a kulle kullen makircinsu na ganin bayan addinin musulunci .
380781