Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na bulletins-electroniques cewa; mnistan ilimi na kasar Holland (Ronald Plasterk) ya bayyana cewa; ma'aikatarsa na da wani shiri na kafa wata cibiyar bincike ta addinin Musulunci a kasar da za a saka wa suna cibiyar bincike kan addinin musuluci. Ya ce babbar manufar kafa wannan cibiya ita ce bayar da dama ga daliban jami'a da suke son su gudanar da bincike kan addinin Musulunci su samu kayayyakin binciken da suke bukata cikin sauki, ta hakan zai taimaka musu wajen gudanar da binciken nasa. Ya ce cibiyar za ta rika koyar da wasu ilmomi na addinin msulunci ga dalbai masu bukatar sanin wannan addini, ya kara da cewa yanzu haka ma'aikatarsa na shirin ware zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan biyu da rabi domin fara gudanar da wannan aiki na gina cibiyar.
380822