Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-dustur) da ake bugawa a birnin Aman na kasar Jordan cewa; ministan kula da harkokin addini na kasar (Abdullafatah salah) ya bayyana cewa; a karo na biyar an kammala bayar da horo ga masu ayyukan isar da sakon muslunci da yada shi a birnin Aman na kasar Jordan. Ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da wannan bayar da horo ga daruruwan mutane da suke da sha'awar su shiga cikin ayyuka na yada sakon addinin Musulunci tare da koyar da mutane addini a aikace, musamman ma ga wadan da basu san addinin Musulunci ba. Ya kara da cewa ana kashe makudan kudi wajen gudanar da wannan aiki mai matukar muhimmanci kuma hakan yana haifar da da mai ido a kowane lokaci, domin ta hakan ne ake samar da limamai, malaman makarantun islamiyya da dai sauransu.
380805