IQNA

A Kasar Suriya An Kaddamar Da Taro Kan Kudus A Matsayin Fadar Al'adu Ta Duniyar Larabawa

Bangaren siyasa da zamantakewa; An fara taro kan birnin Kudus a matsayinsa na fadar al'adu ta kasashen larabawa da hakan ke nuni da matsayinta a tsakanin larabawa.
Daga kasar Surya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin fara wannan taro bayan da ta nakaltto daga majiyar gwamnatin surya Sana cewa;Wannan taro nada matukar muhimmanci ga kasashen larabawa da al'umominsu da kuma yadda wannan birnin mai tsawon tarihi ke nuna muhimmancin gaske. Mahmud Alkhalidi shugaban komitin shirya wannan taro ya bayyana dalilin gudanar da wannan taro da kuma yadda mahalarta wannan taro suka yi marabawa da wannan tunani na shirya wannan taro a kokowar maido da martabar wannan birnin na Kudus mai girma da dokaka.

381002