IQNA

Za A Kaddamar da Gasa Tsakanin Gidajen Littafai A Kasar Labanon

Bangaren al'adu da kwarewa: ofishin da ke kula da yada al'adun kasar Iran ne a kasar ta Labanon ya shirya wannan gasar a daidai lokacin tunawa da shahadar Murtada Mutahhari.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; wannan gasa an shirya ta ne kan littafan da suka shafi rayuwar shahid Murtada Mutahhari da taken tarbiyar musulunci kuma daga cikin yan takara akwai malummai daga makarantu daban-daban na wannan kasa. A makon gobe ne dai za a fara wannan gasar da ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a ketare ya shirya a wannan kasa ta labanon.

381069