Bangaren rahoto: Daraktan cibiyar ilimi ta 'yan sunna da ke garin Kalaleh ya bayyana cewa; sama da mahardatan kur'ani 400 ne suka samu horo a wannan cibiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wata zantawa da ta hada shi da daraktan cibiyar ilimi ta 'yan sunna da ke garin Kalaleh Akram Mash'ufi Samandar ya bayyana cewa; sama da mahardatan kur'ani 400 ne suka samu horo a wannan cibiya. Ya ci gaba da cewa an gina wannan cibiyar ilimi ta Hauza a wanna gari tun sama da shekaru 60 da suka gabata, kuma bat a gushe ba tana ci gaba da horar da dalibai tare da basu ilimi mai zurfi, daga ciki kuwa hard a ilimi karatu da hardar kur'ani mai tsarki, inda ya zuwa yanzu wannan cibiya a cewarsa ta yaye dalibai da suka hardace kur'ani mai tsarki baki dayansa har sama da dalibai 400, wanda ya ce hakan a bin alfahari ne gare su da ma al'ummar garin baki daya. Ya ce yanzu haka akwai dalibai 80 da suke karatu a wannan cibiya a bangaren hardar kur'ani, inda 16 daga cikinsu yanzu haka suna gab da kammala hardar.
380974