Bangaren al'adu da zamantakewa: Shugaban 'yan kasuwar Iran tare da wasu wadanda suke cikin tawagarsa sun kai wata ziyara a babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani a kasar Albania.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; shugaban 'yan kasuwar Iran tare da wasu wadanda suke cikin tawagarsa sun kai wata ziyara a babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani a kasar Albania. Rahoton ya ce shugaban 'yan kasuwa na jamhuriyar musulunci ta Iran tare da jakadan Iran a kasar Albania gami da wasu jami'ai da ke cikin tawagarsa sun kai ziyara a cibiyar ne domin gane wa idanunsu yadda ayyukanta suke tafiya, da kuma zantawa tare da masu kula da cibiyar domin sanin hanyoyin da za su iya bayar da gudunmawa wajen ci gaba da tafiyar da ayyukan cibiyar. Shugaban 'yan kasuwar na Iran ya bayyana matukar jin dadinsa dangane da yadda cibiyar take gudanar da ayyuka na cigaban addinin musulunci, musamman yada sahihiyar fahimta da sako na alkur'ani ga al'ummar kasar, domin su samu cikakkiyar masaniya dangane da addinin musulunci da kuma sakon alkur'ani mai tsarki, ya ce za su taimaka ma wannan cibiya da duk a bin da za su iya domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda take yi a yanzu ko fiye da hakan ma a nan gaba.
380694