IQNA

Dole Ne A Yi Aiki Da Dokokin Musulunci A Birtaniya

Bangaren rahoto: Limamin juma'a na birnin London Jalal Bitaraf ya bayyana cewa; dole a yi aiki da dokoki irin na shari'ar musulunci a kasar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na jaridar (Daily Express) cewa; babban limamin juma'a na birnin London Jalal Bitaraf ya bayyana cewa; dole a yi aiki da dokoki irin na shari'ar musulunci a kasar Birtaniya. Malamin ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar hudubar juma'a masallancin juma'a na birnin London, ya ci gaba da cewa; bisa la'akari da yawan musulmin da suke zaune a kasar Birtaniya da kuma matsayinsu a cikin harkokin na zamnatakewar al'ummar kasar, ya zama wajibi a hukumance a san da zaman shari'ar musulunci da dokokinta, domin kiyaye hakkokin musulmi. Ya ce ana danne hakkokin musulmi da dama wadanda kuma suna da hakkin a kiyaye wadannan hakkoki nasu a kasar Birtaniya, domin kuwa musulmi suna da tsari da addininsu ya tsara musu subi a cikin dukkanin harokin rayuwarsu, suna da halal da haram, kuma za a iya kiyaye musu wadannan ka'idoji nasu a halin yanzu a hukumance a Birtaniya, kuma ya zama waji a yi hakan.

381005