IQNA

Tsarin Jamhuriyar Musulunci Ya Ginu Kan Adalci Da Tsoron Allah

14:26 - March 30, 2009
Lambar Labari: 1758818
Bangaren siyasa da zamantakewa: Tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran ya gine ne kan shika-shikai na adalci da tsoron Allah, kuma dole a kula da wannan bangare mai matukar muhimmanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa, limamin babban masallacin juma'a na birnin Kermansha (Hossein Ibrahimi) ya jaddada cewa; tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran ya gine ne kan shika-shikai na adalci da tsoron Allah, kuma dole a kula da wannan bangare mai matukar muhimmanci. Ya ci gaba da cewa, lamari ne mai matukar muhimmanci al'ummar Iran kama daga masu jagoranci har zuwa wadanda ake jagoranta, su kwana da sanin cewa tsarin musulunci wanda ya ginu kan manufofi na juyin juya halin musulunci, tsari ne wanda ya ginu kan adalci da tsoron Allah, kuma dole kowane bangare na wannan al'umma ya kiyaye hakan a cikin dukkanin harkokinsa, domin wannan a cewarsa wata amana ce ta ubangiji da zai tambayi wadanda ya dora ma ita, kuma kowa ne mutum da ke cikin jamhuriyar musulunci yana dauke da wannan nauyi.


380980





captcha