IQNA

An Sanar Da Sunayen Wanda Suka Yi Nasara A Gasar Darussan Kur'ani

14:24 - March 30, 2009
Lambar Labari: 1758819
Bangaren kur'ani: An sanar da sunayen wadanda suka samu nasara a gasar darussan kur'ani da aka gudanar a ranar 22 ga watan Esfand na shekarar shamsiya da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a jiya Lahadi an sanar da sunayen wadanda suka samu nasara a gasar darussan kur'ani da aka gudanar a ranar 22 ga watan Esfand na shekarar shamsiya da ta gabata. Shugaban cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani sheikh Kara'ati ya bayyana cewa; an gudanar da wannan gasa ne domin karfafa gwiwar masu karatu da hardar kur'ani, inda aka fitar da wasu darussa da ke cikin kur'ani mai tsarki aka gudanar da gasar kansu, kuma an samu halartar masu karatu daga sassa daban-daban na jamhuriyar musulunci ta Iran. Daga cikin muhimman abubuwan da gasar ta mayar da hankali kansu kuwa akwai kissoshin annabawa, da kuma tarihin kira zuwa ga Allah gami da sanin makomar wadnda suka karba kiran ubangiji daga annabawa, da kuma sanin makomar wadanda suka karyata kiran annabawa.

380903


captcha