IQNA

'Yan Mata 350 Suka Yi Bikin Isa Takalifi A Hubbaren Imam Hussain (AS)

Bangaren rahoto: An gudanar da bikin cikar 'yan mata 350 shekarun takalifi a hubabren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Kheimah cewa; an gudanar da bikin cikar 'yan mata 350 shekarun takalifi a hubabren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma. Daya daga cikin wadanda suka halarci taron Sheikh (Abdulrida Mu'adh) ya bayyana cewa; cibiyar kula da ayyukan alhairi ta Kheimah ita ce ta dauki nauyin gudanar da bikin, inda 'yan mata 350 da suka isa shekarun takalifi suka halarci hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin a cikin suturar musulunci, inda dukkaninsu suka saka hijabi da ya rufe jikunnasu baki daya. A wurin taron an gabatar da jawabai kan muhimmancin rawar da mata ke takawa wajen tarbiyantar da iyali bisa tarbiya da ta ginu kan koyarwar addinin musulunci da shari'arsa, wanda kuma hakan nauyi da ya rataya kan dukkanin bangarorin biyu maza da mata, amma kasantuwar mata sun e suka fi kusa da iyali rawar da suke takawa ta dara ta maza, a kan haka wajibi su san hanyoyin tarbiya bisa koyarwa ta addinin musulunci, domin samara da iayalai na gari.

381369