IQNA

Dole Ne Mabiya Mazhabar Shi'a Su Yi Koyi Da Ahlul Baiti A Aikace

Bangaren rahoto: Ayatollah Shirazi ya jaddada cewa dole ne mabiya tafarkin ja'afariyya su yi koyi da ahlul bait a cikin dukkanin ayyukansu, wanda hakan shi n eke tabbatar da cewa suna bin sahihin tafarki na koyarwar iyalan gidan manzon Allah (SAW)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar Kheimah cewa, wata tawaga daga birnin Isfahan ta kai ziyara ga Ayatollah Shirazi daya daga cikin manyan malaman addini da ake komawa zuwa gare su a birnin Qom da ke jamhuriyar musulunci ta Iran, inda Ayatollah Shirazi ya jaddada cewa dole ne mabiya tafarkin ja'afariyya su yi koyi da ahlul bait a cikin dukkanin ayyukansu, wanda hakan shi n eke tabbatar da cewa suna bin sahihin tafarki na koyarwar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a cikin bayanin da ya yi wannan tawaga babban malamain ya kawo wasu daga cikin ayoyin kur'ani mai tsarki da ke nuni da wajabcin yin koyi da manzon Allah a cikin ayyuka da dabi'u, wanda kuma koyi da manzon Allah yana nufin koyi ne da iyalan gidansa, kamar yadda koyi da iyalan gidansa koyi da shi. Ya ce bin tafarkin manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka shi ne sahihin tafarki da ke kai mutum zuwa madaukakiyar daraja a wajen Allah madaukakakin sarki. Ya kara da cewa mabiya mazhabar shi'a da suke kira zuwa ga bin sahihin tafarkin manzo da iyalan gidansa, wajibi ne a ga aikin manzo tare da iyalan gidansa a cikin ayyukansu.

381367