Bangaren fikira da ilimi: Mafi muhimmancin abin komawa zuwa gare shi wajen sanin abubuwan da suka wakana shi ne tarihi, wannan shi ne ya sanya musulmi suka zama kangaba wajen bin diddigin tarihi domin sanin hakikanin abubuwan da suka wakana, ta yadda hakan zai basu dammar sanin koyarwar manzo (SAW) da ta ciyar da rayuwar dan adam gaba.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna tare da wani dalibin jami'ar Ahvaz da ke karatun digiri na uku a fagen ilimin falsafa ya bayyana cewa; abin da ked a matukar muhimmancin kuma abin komawa zuwa gare shi wajen sanin abubuwan da suka wakana shi ne tarihi, wannan shi ne ya sanya musulmi suka zama kangaba wajen bin diddigin tarihi domin sanin hakikanin abubuwan da suka wakana, ta yadda hakan zai basu dammar sanin koyarwar manzo (SAW) da ta ciyar da rayuwar dan adam gaba. Ya ce manzon Allah (SWA) shi ne ya kawo wa 'yan adamtaka dukkanin ci gaba ta fuskacin ilimi da zamantakewa, wanda kuma hakan shi ne ya ba musulmi dammar shiga gaba a cikin lamurra da dama bisa riko da koyarwar manzonsu, domin shi ne abin komawa zuwa gare shi na farko a cikin lamurra, shi ne tushen ilimin dan adam da ci gabansa.
379520