Bangaren adabi: Za a bude kasuwar baje kolin littafai a karo na ashirin da biyu daga ranar 16 zuwa 26 ga watan Ordibehesht hijira shamsiya a masallacin Imam Khomeni da ke birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren kula da huldar jama'a na cibiyar da ke kula ayyukan baje kolin kayyakin al'adu da ilimi a Iran cewa; za a fara gudanar da kasuwar baje kolin littafai a karo na ashirin da biyu daga ranar 16 zuwa 26 ga watan Ordibehesht hijira shamsiya a masallacin Imam Khomeni da ke birnin Tehran. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka ana ci gaba da samara da manyan dakunan da za a baje kolin littafan a cikinsu a wannan katafaren masallaci, wanda kuma wannan shine karo na uku da za a gudanar da irin wannan kasuwar baje kolin littafai a masallacin. Yanzu haka dai cibiyar da ke kula da ayyyukan baje kolin kayayyakin al'adi da ilimi a Iran ta fara rijistar kamfanoni da cibiyoyi gami da mu'assasosin da za su kawo littafansu a wurin, kama daga cikin gida har zuwa wajen kasar, kamar yadda take ci gaba da gudanar da ayyukan da suka kamata kafin lokacin fara kasuwar bajen kolin.
381374