Bangaren siyasa da zamantakewa: Babban malamamin addinin nan na kasar Labanan Sayyid Muhammad Husseini Fadlollah, ya kirayi kafofin yada labarai na kasashen musulmi da na larabawa da ma dukkanin masu 'yanci a duniya, da su hada dukkanin bayanai da ke tabbatar da wajabcin gurfanar da Isra'ila ga shari'a, domin wayar da kan al'ummomin duniya kan hakan musamman ma na yammcin turai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna a reshensa da ke kasar Labanan ya habarta cewa; fitaccen malamamin addinin nan na kasar Labanan Sayyid Muhammad Husseini Fadlollah, ya kirayi kafofin yada labarai na kasashen musulmi da na larabawa da ma dukkanin masu 'yanci a duniya, da su hada dukkanin bayanai da ke tabbatar da wajabcin gurfanar da Isra'ila ga shari'a, domin wayar da kan al'ummomin duniya kan hakan musamman ma na yammcin turai. Malamin ya ce abin yahudawan sahyuniya suke yin a kisan kiyashi a kasashen larabawa musamman ma a palastinu dalili ne da za a hukunta su a gaban shari'a, kamar yadda abin da suka aikata na kisan gilla kan al'ummar Gaza a cikin 'yan lokutan nan ya isa ya zama babban dalili da ke tabbatar da cewa yahudawan sahyuniya su ne mafi munin al'umma a doron kasa.
381359