IQNA

Jam'iyar Masu Kishin Musulunci Ta Yi Nasara A Zaben Turkiya

14:23 - March 31, 2009
Lambar Labari: 1759266
Bangaren siyasa da zamantakewa: Sakamakon farko da aka sanar na zabukan gundumomi da aka gudanar a kasar Turkiya na nuni da cewa jam'iyar da ke mulki a kasar ta masu kishin islama ita ce kan gaba wajen samun sakamako mai rinjaye.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reuters cewa; sakamakon farko da aka sanar na zabukan gundumomi da aka gudanar a kasar Turkiya na nuni da cewa jam'iyar da ke mulki a kasar ta masu kishin islama ita ce kan gaba. Rahoton ya ci gaba da cewa an gudanar da zabukan ne gundumomin kasar da nufin zaben 'yan majalisar larduna da kuma na gundumomi, inda jamiyar Adalci da ci gaba karkashin jagorancin Rajab tayyib Aurdugan ta yi wa sauran jam'iyun fintinkau. Jam'iyar mai mulki ta samu kashi 39 da digo 12 cikin dari na kuri'un da aka kada, yayin da jam'iyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta samu kashi 23 cikin dari, sai kuma masu kishin kasa ta samu kashi 16 da digo 22 cikin dari. Sakamakon zaben na nuni ne da irin farin jinin da jam'iyar da ke mulki a kasar ked a shi ne, musamman ma pira ministan kasar Rajab Tayyib Ardugan.

381338



captcha