IQNA

Tarbiyar Annabawan Ta Ginu Kan Wa'azi da Bushara

14:36 - March 31, 2009
Lambar Labari: 1759270
Bangaren fikira da ilimi: A mahangar kur'ani mai tsarki tarbiyar annabawa ga baki daya ta ginu ne a kan wa'azi da bushara, wanda kuma za a iya fahimtar hakan a cikin ayoyin Allah da dama idan aka warware ma'anarsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna daga reshensa na lardin Azarbaijan ya habarta cewa; bisa mahangar kur'ani mai tsarki tarbiyar annabawa ga baki daya ta ginu ne a kan wa'azi da bushara, wanda kuma za a iya fahimtar hakan a cikin ayoyin Allah da dama idan aka warware ma'anarsu. Bayanin ya cid a cewa addinin musulunci addini ne day a ginu kan akida tabbatatta dab a ta canjawa, kamar yadda tarbiyar da ta ginu kan koyarwarsa ba ta canjawa, wanna ne ya sanya dukkanin annabawa wadanda sun samu tarbiya ne tun a rayuwarsu ta kuruciya a kan akida ta imani da Allah, kuma wannan wani tabbataccen lamari ne da ba ya canjawa.

381384
captcha