IQNA

Matakan Imani A Mahangar Kur'ani

14:36 - March 31, 2009
Lambar Labari: 1759271
Bangaren fikra da ilimi: Imani na da matakai da mutum kan hau, duk matakin da mutum ya hau yana isa zuwa ga wata daraja da matsayi na musamman da zai kashi ga samun aljannar, kuma kur'ani ya yi bayani kan wadannan matakai da daraja daki-daki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna a reshensa na Azarbaijan ya habarta cewa; imani da Allah madaukakakin sarki na da matakai da mutum kan hau, duk matakin da mutum ya hau yana isa zuwa ga wata daraja da matsayi na musamman da zai kashi ga samun aljannar, kuma kur'ani ya yi bayani kan wadannan matakai da daraja daki-daki. A cikin bayanai na ma'anonin ayoyi da suke bayyana matakan imani da ke mutum zuwa ga daraja da samun yardar Allah, akwai natsuwa da yarda abin da Allah ya rubuta wa bawa, tare da mayar da komai ga Allah ba tare da damuwa da hukuncinsa, wato yarda da Allah a matsayin ubangiji mai iko da bawa da duk abin da ke tattare da shi, tare da kaskantar da kai ga ubangiji da bin umurninsa a cikin dukkanin lamurra, tare da hanuwa daga dukkanin abubuwan da ya yi hani kansu.


381381



captcha