IQNA

An Gudanar Da Taron Mako Guda Da Rasuwar Matar Imam Khomeini (RA)

Bangaren rahoto: An gudanar taron cika mako guda da rasuwar maid akin marigayi Imam khomeni (RA) garin Herand, wanda ya samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na kasar Iran.
Kamfanin dillancin lbaran Ikna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin yada addini reshen lardin Isfahan cewa; an gudanar taron cika mako guda da rasuwar maid akin marigayi Imam khomeni (RA) garin Herand, wanda ya samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na kasar Iran musamman ma daga yankunan lardin Isfahan. Shugaban cibiyar kula da ayyukan yada addini a reshen Isfahan Hojjatol Islam (Mradi) ya bayyana cewa; a wajen taron an gabatar da jawabai da suka danganci irin rawar da marigayiya (Khadija Saqfi) ta taka wajen mara wa Imam khomeni baya a dukkanin gwagwarmayar da ya yi har zuwa cin nasara, da ma bayan samun nasar juyin juya halin musulunci. Kamar yadda wasu daga cikin jami'an gwamnati da suka santa tsawon lokaci gami da wasu malamai da suka kasance tare da Imam a lokacin gwagwarmaya da ma bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci, suka tabbatar da cewa ta kasance mace ce mai iamni da hakuri gami da tawakkali ga ubangiji, kamar yadda ta kasance mai karfin zuciya, inda take karfafa Imam a kowane lokaci a cikin dukkanin lamurransa na gwagwarmaya.

381549