IQNA

Muhimmancin Masallatai Wajen Tarbiyantar Da Matasa

15:45 - April 01, 2009
Lambar Labari: 1759409
Bnagaren siyasa da zamantakewa: Masallaci wuri ne mai matukar muhimmanci wajen yada koyarwar musulunci, tare da wayar da kan jama'a kan mahangar musulunci dangane da lamurran siyasa da zamantakewa da dai sauransu, kamar yadda wuri ne na dora matasa kan sahihiyar tarbiya ta addinin musulunci.
A wata zantawa da ta hada kanfanin dillancin labaran Ikna da malama (Afsaneh Mosavi) wata masaniya kan harkokin zamantakewa ta bayyana cewa; masallaci wuri ne mai matukar muhimmanci wajen yada koyarwar musulunci, tare da wayar da kan jama'a kan mahangar musulunci dangane da lamurran siyasa da zamantakewa da dai sauransu, kamar yadda wuri ne na dora matasa kan sahihiyar tarbiya ta addinin musulunci. Ta ci gaba da cewa masallaci ba wuri ne na yin salla ko karanta addu'oi ba kawai, a a wuri ne da ke muhimmanci da za a iya kiran shi na ibada da yada al'adun musulunci, a lokaci guda kuma makaranta, domin kuwa a lokacin ma'aiki masallaci nan wurin gudanar da dukkanin harkokin yada addini tare da bayyana manufofin wahayin ubangiji, a kan haka ya zama wajibi musulmi su kara fahimtar cewa masallaci wuri na gudanar da dukkanin harkokinsu na addini, kama daga harkokin siyasar addini har zuwa rayuwa ta zamantakewa, yadda da za su yi daidai da koyarwar musulunci.

381396







captcha