IQNA

Ranar 12 Ga Watan Farvardin Aka Kafa Tsarin Musulunci A Iran

15:43 - April 01, 2009
Lambar Labari: 1759410
Bnagaren siyasa da zamnatakewa: Ranar 12 ga watan Farvardin rana ce da aka kafa tsarin musulunci a Iran, bayan amincewar sama da kashi 98 cikin dari na al'ummar Iran da hakan.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da babban malami kuma limamin masallancin juma'ar birnin Behshar Hojjatol islam (Sayyid Saber jabbari) ya bayyana cewa; ranar 12 ga watan Farvardin rana ce da aka kafa tsarin musulunci a Iran, bayan amincewar sama da kashi 98 cikin dari na al'ummar Iran da hakan. Malamin ya ci gaba da cewa bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran da watanni biyu, an bayar da dama ga mutanen kasar da su zabi irin tsarin da suke bukata ya jagorance su, inda sama da kashi 98 cikin na al'ummar Iran suka amince da tsarin musulunci karkashin jagorancin marigayi Imam Khomeini, lamarin da ya bayar da damar gudanar da zabukan 'yan majalisun dokoki, da majalisar kwararru masu zabar jagora gami da zaben shugaban kasa. Daga lokacin kuma jamhuriyar musulunci ta ci gaba da tafiya kan tsarin addinin musulunci kamar yadda al'ummar kasar suka zaba.

381511
captcha