IQNA

Addinin Musulunci Ya Yi Wasiyya Da Sada Zumunci

15:44 - April 01, 2009
Lambar Labari: 1759411
Bangaren siyasa da zamantakewa: A ranar idin Nouroz ana girmama al'adu da koyarwa irin ta addini, wanda kuma wajibi ne ga dukkanin masu gudnar da bukukuwan murnar ranar idin nouroz su kiyaye al'adu na musulunci ba tare da aikata abubuwan da Allah ya yi hani kansu ba.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da shugaban cibiyar yada addinin musulunci da al'adu bisa koyarwar musulunci reshen garin Tafrash, Hojjatol islam (Davud Jomani) ya bayyana cewa; a ranar idin Nouroz ana girmama al'adu da koyarwa irin ta addini, wanda kuma wajibi ne ga dukkanin masu gudnar da bukukuwan murnar ranar idin nouroz su kiyaye al'adu na musulunci ba tare da aikata abubuwan da Allah ya yi hani kansu ba. Ya ci gaba da cewa a kowane lokaci koyarwar addinin musulunci ita ce kan gaba a wurin musulmi, kamar yadda al'adu da addinin musulunci ya amince da su su ne kan gaba a kan dukkanin wasu al'adu, ya ce a lokacin da ake gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar farisawa, ya zama wajibi a guji duk wasu al'adu da suka yi hannun riga da koyarwa irin ta manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka, wannan shi ne zai mayar da tarukan su zama bisa koyarwar addini da kuma ibada.

381423


captcha