Bangaren siyasa da zamantakewa:A ranar sha biyu ga watan farvardin ne a nan Iran aka fara kaddamar da tsarin musulunci a wannan kasa inda duniya ta kasance tare da wani sabon yanayi mai muhimmanci a rayuwa da addini.
Daga birnin Qum ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin cewa: komitin tuntubar juna a cibiyar yada addinin musulunci a wannan birni ta fitar da wani bayani da a cikinsa take bayyana muhimmancin wannan rana ta sha biyu ga watan Farvardin ran ace babba ta nasarar juyin juya halin musulunci domin kuwa a wannan ran ace al'ummar Iran suka nuna fatarsu da zabinsu na tsari irin na Musulunci da zai zama jagora a rayuwarsu duniya da lahira tare da nunawa duniya abin da suka zaba a rayuwa da addininsu.
381738