Bangaren al'adu da fasaha: Bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a iran mata sun samu gagarumin ci gaba ta fuskacin rubuce-rubuce.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; shaharriyar marubuciyar nan ta Iran (Raziyeh Najjar) a lokacin da take mayar da martini kan wani jawabi dangane da canje-canjen da aka samu a Iran ta fuskacin rubuce-rubucen zamani, musamman ma rawar da mata suke takawa kan hakan, ta bayyana cewa mata a Iran sun samu ci gaba fiye da dukkanin zamunan da suka gabata a Iran ta fuskacin rubuce-rubuce bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran. Marubuciyar ta bayyana hakan ne a wajen taron baje kolin littafi karo na uku da ake gudanarwa a birnin Ankara na kasar Turkiya. T aci gaba da cewa za a iya cewa a wasu bangarorin ma mata sun fi maza taka gagarumar rawa ta fuskacin rubuce-rubuce, wannan kuma ya samo asali ne daga irin tunanin marigayi Imam Khomeini (RA)
Wannan dai shi ne karo na uku da ake gudanar da irin wannan baje kolin littafi a Turkiya, kuma an gayyaci Iran a matsayin babbar bakuwa a taron.
381854