IQNA

An Gudanar Da Taron Kan Mahangar Magabata Dangane Da Hadin Kan Musulmi

16:05 - April 02, 2009
Lambar Labari: 1759492
Bangraen siyasa da zamntakewa : An gudanar da wani taro na kasa da kasa a babban dakin taron oten din Galria da ke birnin Beirut na kasar Labanan, domin yin nazari kan mahamngar manyan malaman nan biyu da suka gabata a Labanan sheikh (Abdullah Al'alayili) da kuma sheikh (Jawad Mogniyah) kan sabunta tunani da mahanga da kuma hadin kan muaulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; A farkon taron shugaban kwamitin larabawa da musulmi da ke shiga tsakani wajen tattaunawa da bangarorin mabiya addinin kirista (Riyad JuJur) ya gabatar da makala mai take (Kusanto da addinai) a cikin makalar ya bayyana muhimmancin da ke tattare da kusanto fahimta tsakanin addinai musamman ma addinin musulunci da kuma addinin kiristanci, wadanda dukkaninsu addinai biyu da aka safkar daga sama, ya ci gaba da cewa dukkanin addinan biyu na musulunci da kiristanci babbar manufarsu ita ce shiryar dad an adam zuwa ga abin da yake daidai a cikin rayuwarsa, saboda haka addinan biyu suna dauke da manufofi na fahimtar juna da sulhu da adalci, da kuma daukaka dan adam zuwa matsayi madaukaki,ya ce babu wani dalili da zai hana mabiya wadannan addinai biyu fahimtar junansu tare da kusanto da manufofinsu, domin kuwa duk wani shiri na raba kan mabiya addinan biyu ba ya rasa nasaba da makircin yahudawan sahyuniya, da kuma 'yan korensu daga cikin gwamnatocin kasashen yammacin turai.

381767
captcha