Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habrta cewa; jaridar (Rising Kashmir) da ake bugawa a kasar India, ta bada wani rahoto da ke cewa ana ci gaba da adana wani kur'ani da aka danganta da Imam Kazim (AS) a birnin Srinagar na kasar ta India. Jaridar ta buga takaitaccen labari dangane da yadda wannan kur'ani ya isa yankin Kashmir na kasar India, inda ta bayyana cewa an bada labarin cewa; Imam Kazim (AS) yana tare da wannan kur'ani a lokacin da Khalifa Harun Rashid ya tsare shi a gidan kaso, bayan da ya yi shahada sai aka dauki kur'anin zuwa birnin Ardabil na kasar Iran, daga nan kuma a cikin shekara ta 665 bayan hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina wani mutum mai suna (Sayyid Sultan Gabrawi) ya dauki kur'anin zuwa Kashmir, a s cikin shekara ta 1968 miladiyya aka gina wani wuri na musamman inda aka ajiye shi, daga bisani kuma aka kafa wani kwamiti da zai rika kula da adana wannan kur'ani.
382211