Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na kungiyar OIC cewa; gwamnatin kasar Libya za ta dauki nauyin bakuncin taron kungiyoyin farar hula na kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da za a gudanar a karo na biyu a birnin Tripoli fadar mulkin kasar. Bayanin ya ce sama da kungiyoyin farar hula na kasashen musulmi mambobi a kungiyar OIC ne za su halarci taron na birnin Tripoli, inda za su yi bitar muhimman abubuwan da suka tattauna kansu a zamansu na farko a birnin Dakar na kasar Senegal, wanda suka gudanar a gefen taron kungiyar OIC na goma sha shida a cikin watan Maris din shekara ta 2008.
Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce samar da hanyoyin da za a rika taimaka ma al'ummomin musulmi marassa galihu a ko'ina suke cikin fadin duniya.
382105