Bangaren rahoto: A cikin littafin imani da hankali na shugaban cibiyar yada addinin Musulunci ta birnin Hamburg na kasar Jamus Sayyid Abbas Hussaini, an ambaci wasu daga cikin rubuce-rubucen tsohon farfesan nan na kasar Austria Hobartos Minarc.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta birnin Hamburga na kasar Jamus cewa; a cikin littafin imani da hankali na shugaban cibiyar yada addinin Musulunci ta birnin Hamburg na kasar Jamus Sayyid Abbas Hussaini, an ambaci wasu daga cikin rubuce-rubucen tsohon farfesan nan na kasar Austria Hobartos Minarc, wanda ya shahara ta fuskacin ilimin falsafa, wanda kuma ya taka wara wajen wayar da kan al'ummomi musamman ma na yammacin turai da ba su san addini ba ko kuma ma ma manufar halittarsu baki daya, inda ya tabbatar da cewa hankali dan adam a kowane lokaci yana jansa zuwa ga abin da ke daidai, amma faragar da ke cikin hankalin wadda za ta iya maye gurbin shirya ta kan rinjayi dan adam da tunaninsa a wasu lokuta. Shugaban cibiyar addinin Musulunci ta Hamburg, ya kawo misalai da dama daga magnganun wannan farfesa, a cikin littafinsa da ya rubuta domin mayar da martani ga mahangar paparoma Benedict na 16 kan addinin Musulunci.
382145