Bangaren al'adu da fasaha: An buga tare da yada littafin tarihin rayuwar ma'aiki (SAW) a kasar Jamus, bayan da aka fassara shi a cikin harshen jamusanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; wannan littafin wani bangare ne na rayuwar ma'aiki wanda Shahid Mottahari ya rubuta a cikin harshen farisanci, amma wasu cibiyoyin kula da harkokin addinin Musulunci a kasar Jamus sun dauki nauyin fassara littafin zuwa harshen jamusanci domin yada shi ga al'ummar kasar, wanda hakan kuma na daya daga cikin salon nuna wa al'ummar kasar ta jamus sahihiyar mahangar addinin Musulunci ne, ba irin fahimtar da aka cusa cikin kwakwalensu dangane da addinin Musulunci ba.
Bayanin ya kara da cewa littafin an fassara shi da harshen jamusanci inda ya kai shafi 130, kuma yanzu haka za a iya samunsa a kasuwannin littafai a kasar Jamus.
382132