IQNA

An Buga Littafain Muhimmancin Sallar Juma'a A Mahangar Imam Ali (AS)

Bangaren fikira: An buga littafin muhimmancin sallar Juma'a da ladubbanta a mahangar Imam Ali (AS) wanda Hojjatol Islam Mofid Fayyadi ya rubuta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; madaba'antar masallacin jamkaran ta buga littafin muhimmancin sallar Juma'a da ladubbanta a mahangar Imam Ali (AS) wanda Hojjatol Islam Mofid Fayyadi ya rubuta.rahoton ya ce manufar buga littafin ita ce bayyana mahangar Imam Ali (AS) danagne da muhimamncin da ke tattare da sallar juma'a da kuma ladubbanta, da hakan ya hada da manufofi na ibada da kuma siyasa da ke kunshe a cikin sallar Juma'a. A bangaren farko na littafin marubucin ya bayyana matsayin juma'a a mahangar Imam Ali (AS) da muhimamncin tsayar da sallar juma'a kanta, da kuma ladubban halartar sallar. A bangare na biyu kuma ya kawo abin day a hau kan majibncin lamurran musulmi dangane da batun tsayar da sallar juma'a a halin fakuwar ma'asumi.

382137