Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga jaridar )Al-dastur) cewa; Tashar radiyon FM ta kasar Jordan ta sanar cewa nan ba da jimawa ba za ta bude wani bangarenta da zai rika watsa shirye-shiryen kur'ani ta hanyar internet mai suna rayuwar kur'ani. Rahoto ya kara da cewa yanzu haka an kammala mafi yawan shirye-shiryen da suka kamata wajen gudanar da wannan aiki, daga ciki kuwa hard a samar da manyan dakunan watsa shirye-shiryen radiyon, tare da hada muhimamn kayan aiki da suka hada da na'urorin watsa shiri, na'urori masu kwakwalwa, kayan daukar shiri da dai sauransu, kuma za a bude shafin internet wanda zai rika watsa shirye-shiryen tashar kai tsaye, tare da bayar da dukkanin bayanai kan shirye-shiryenta, wasu a cikin sauti wasu kuma a rubuce, kamar yadda za a iya kama tashar kai tsaye a kan tauraron dan adam. Rahoton ya kara da cewa manufar bude tashar dai ita ce yada koyarwa irin ta kur'ani tsakanin al'ummar musulmi musamman ma dai matasa.
382127