IQNA

2- Hukumar Kare Al'adu Da Binkasa Ulimi Ta Majalisar Dinkin Duniya Zata Halarci Taron OIC

Bangaren kasa da kasa: hukumar kula da ilimi da al'adu ta majalisar dinkin duniya za ta halarci taron da kungiyar kasashen musulmi za ta shirya kan tattalin arziki da al'adu a musulunce.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga hukumar da ke kula da ilimi da al'adu ta majalisar dinkin duniya ta watsa rahoton cewa: hukumar ta bayyana aniyarta ta halartar taron da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya kan tattalin arziki da al'adu .Muhammad Algamari ne shugaban hulda da jama'a da kuma tuntubar juna a wajen hukumar ya bada wannan labari na halartar hukumar a taron da kungiyar kasashen musulmi za ta shirya a nan gaba kan al'adu da tattalin arziki.

382103