Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; an kawo karshen zaman taron da kungiyoyin farar hula na kasashe mambobi a kungiyar OIC suka gudanar a birnin Tripoli na kasar Libya, rahoton ya kara da cewa dukkanin wakilan kungiyoyin farar hula da suka halarci taron sun jaddada wajabcin samar da ofishin hadakar kungiyoyin farar hula na kasashen OIC. Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyoyin farar hula na kasashen musulmi suka gudanar da zamansu, tun bayan da suka gudanar da irin wannan zama karo na farko a birnin Dakar na kasar Senegal a cikin watan Maris din shekara ta 2008, a lokacin da shugabannin kasashen kungiyar hadin kan musulmi ta OIC din suka gudanar da babban taronsu.
382394