Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani taro na kasa da kasa a jami'ar birnin paris na kasar Faransa a cikin watan Aprilun nan da muke ciki, kan Musulunci da Ijtihadi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saphrnews cewa; za a gudanar da wani taro na kasa da kasa a jami'ar birnin paris na kasar Faransa a cikin watan Aprilun nan da muke ciki, kan Musulunci da Ijtihadi.Bangaren karatun shari'a na jami'ar Paris shi ne zai dauki nauyin bakuncin taron, wanda zai samu halartar masana daga kasashe daban-daban da suka hada da kasashen turai, kamar yadda wasu malaman jami'a daga kasashen Algeria, Saudiyya, Masar, Haddadiyar daular larabawa, Labanan, Morocco Sudan da dai sauransu, inda za su gabatar da makaloli a wajen taron.
382420