Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Nasij cewa; ofishin jakadancin kasar Kuwait a kasar Belgium zai dauki nauyin gudanar da gasar karatun kur'ani mai taken gasar Sabah Ahmad Jabir Sabah a birnin Brussel fadar mulkin kasar Belgium. Jakadan kasar Kuwait a kasar ta Belgium shi ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa babban masallacin birnin Brussel shi ne zai gudanar da gasar wadda ofishin jakadancin Kuwait zai dauki nauyinta, inda musulmi daga mazauna kasar ta Belgium daga sassa daban-daban za su halarta. Ya kara da cewa ofishin jakadancin Kuwait a kowane lokaci na kokarin hada musulmin kasar Belgium wajen gudanar da taruka na addini, kasantuwar su ne marassa rinjaye a kasar.
382426