IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Taswirar Kasashen Larabawa Da Na Musulmi

12:57 - April 05, 2009
Lambar Labari: 1760468
Bangaren kasa da kasa: Za a bude taron masana daga kasashen larabawa da na musulmi kan taswirar kasashen musulmi da na larabawa a birnin Demascus na kasar Syria.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SAN Ana kasar Syria cewa; a yau lahadi za a bude taron masana daga kasashen larabawa da na musulmi kan taswirar kasashen musulmi da na larabawa a birnin Demascus fadar mulkin kasar ta Syria. Rahoto ya ci gaba da cewa babbar manufar wannan taro ita ce sake farfado da batun taswirar kasashen musulmi da na larabawa, inda masana daga kasashen duniya har ma daga kasashen yammacin turai za su samu halartar taron domin gabatar da makalolin da suka rubuta kan hakan, tare da bayyana mahangar al'ummomin duniya dangane da musulmi da larabawa a dukkanin nahiyoyin duniya. Bangaren yaruka na jami'ar Demascus shi ne zai dauki nauyin gudanar da taron.

382463


captcha