IQNA

Tafsirin Da Ake Dangantawa Da Imam Askar (AS) Ya Kumshi Kololuwar Sani

12:55 - April 05, 2009
Lambar Labari: 1760471
Bangaren Nazari: Tafsirin da ake dangantawa da imam Hasan Askari (AS) duk da cewa dalilin da ke nuni da hakan mai rauni ne amma ya kumshi kololuwar sani domin akwai abubuwa da har yanzu ba a kai ga saninsu ba.
Hujatul islama da musulumi Ali Nasiri mamba a komitin ilimi da tunani wato nazari da al'adu na musulunci a wata hira da cibiyar da ke kula harkokin kur'ani a Iran Ikna dangane da tafsirin da ake danganta shi da Imam Hasan Askari (AS) ya bayyana cewa: hadarat ma'asumai (AS) a yawaicin lamura sun kaucewa danganta su da rubuta wani tafsirin kur'ani kai tsaye.Ya kara da cewa; daya daga cikin dalilin day a sa imamai (AS) suke kaucewa fassarar kur'ani kai tsaye shi ne gudun harrafa yawaicin gaskiyar abubuwan da ake nufi kuma ta haka yawancin musulmi su kaicewa hanya da fadawa cikin bata da tabewa.


382468
captcha